1 Timothy 6

1Bari duk wadanda ke bayi a karkashin karkiya su ga iyayengijinsu sun cancanci dukan daraja. Su yi haka domin kada a sabawa sunan Allah da koyarwarsa. 2Bayin da suke da iyayengiji da ke masu ba da gaskiya kada su rena su saboda su ‘yan’uwa ne. A maimakon haka, su yi masu hidima da kwazo. Gama iyayengijin da suke cin ribar aikinsu masu bi ne, kaunattatu kuma. Ka koyar ka kuma bayyana wadannan abubuwa.

3Idan ya kasance wani na koyar da wani abu dabam bai kuma yarda da amintaciyar koyarwa ba, wato maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu. Alal misali ba su amince da koyarwa da ke kai ga Allahntaka ba. 4Wannan mutum mai girman kai ne, kuma bai san komai ba. A maimakon haka, yana da matukar jayayya da gardama game da kalmomi. Wadannan kalmomi na kawo kishi, da husuma, da zage-zage, da miyagun zace-zace, da 5yawan rashin jituwa tsakanin mutane masu rubabbun hankula. Sun bijire wa gaskiya. Suna tunani cewa ibada hanya ce ta yin arziki.” Ka zame daga wadannan abubuwa.

6Yanzu bin Allah tare da dangana babbar riba ce. 7Gama ba mu kawo komai a duniya ba, ba zamu iya fita cikinta da komai ba. 8A maimakon haka, mu dangana da abinci da kuma sutura.

9To wadanda ke son zama mawadata su kan fada cikin jaraba, cikin tarko. Suna fadawa cikin abubuwan wauta da sha’awoyi masu illa da kowanne abu da ke sa mutane su dulmaya cikin lallacewa da hallaka. 10Gama son kudi shine tushen kowacce irin mugunta. Wadansu mutane garin neman kudi sun kauce daga bangaskiya, sun kuma jawowa kansu bakin ciki mai yawa.

11Amma kai, mutumin Allah, ka guji wadannan abubuwa, ka bi adalci, ibada, aminci, kauna, jimiri, da tawali’u. 12Ka yi fama, fama mai kyau na bangaskiya. Ka kama rai madawami da aka kira ka gare shi. A kan wannan ne ka ba da shaida a gaban shaidu masu yawa game da abin da ke da kyau.

13Ina ba ka wannan umarni a gaban Allah wanda ke rayar da dukan abubuwa, da gaban Almasihu Yesu, wanda ya fadi abin da ke gaskiya ga Bilatus Babunti. 14Ka bi doka daidai, babu abin zargi har bayanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

15Allah zai nuna bayyanuwarsa a daidai lokaci- Allah, mai albarka, Makadaicin iko, Sarkin da ke sarauta, Ubangiji mai mulki. 16Shine kadai marar mutuwa, mai zama cikin hasken da ba ya kusantuwa. Ba wanda ke ganinsa, ko ya iya hango shi. Girma ya tabbata a gare shi da kuma madawwamin iko. Amin.

17Ka gaya wa masu dukiya a cikin wannan duniya kada su daga kai, kada su sa bege ga arziki mara dawwama. Maimamakon haka, su sa begensu ga Allah wanda ke ba mu wadatar gaske domin jin dadin mu. 18Gaya masu su yi nagarta su arzurta a ayyuka nagari, su zama masu bayarwa hannu sake. 19Ta haka za su ajiye wa kansu harsashi mai kyau kan abin da ke zuwa domin su amshi rayuwa ta kwarai.

20Timoti, ka kare abin da aka ba ka. Ka nisanci maganar wauta da gardamomin da ke sabawa juna wanda ake kira ilimi a karyace. 21Wadansu mutane suna shelar wadannan abubuwa, don haka sun kauce wa bangaskiyar. Bari alheri ya kasance tare da kai.

Copyright information for HauULB